An kashe mutane 55 a rikicin Kaduna – ‘Yan Sanda

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta bayyana cewar akalla mutane 55 sun rasa rayukan su a wani rikici da ya barke a jihar.

Gwamnatin jihar ta Kaduna ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a garin Kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kajuru ta Kudancin jihar bayan wani rikici da ya barke a garin.

Rikicin dai ya barke ne a jiya Alhamis lokacin da kasuwar garin ke ci. Wadansu rahotanni na cewa adadin mutanen da suka mutu ya zarta hakan.

Wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa ya shaida wa BBC cewa “muna tsaka da cin kasuwa kawai sai wasu matasa da dama sun yi kaurin suna wajen ta da irin wadannan fituntunu, suka fado cikin jama’a da doke-doke suna karya rumfuna suna jidar kayan jama’a.”

310total visits,2visits today


Karanta:  Gyaran Kundun Tsarin Mulki: Majalisar Wakilai ta amince da rage shakarun takara

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.