An Kashe Sojojin MDD 2 a Mali

Hukumar da ke kula da ayyukan samar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali tace sojojinta guda biyu sun mutu yayin da wasu biyu kuma suka samu raunuka bayan motarsu ta taka nakiya

Sanarwar hukumar ta ce motar sojin ta gamu da hadarin ne a garin Aguelhok da ke da nisan kilomita 15 daga garin Kidal.

Mali ta dade tana fama da hare haren ‘yan tawaye da ‘yan ta’adda masu alaka da Al-Qaeda.

Majalisar Dinkin Duniya na da sojoji 11,000 da ‘Yan Sanda 1,700 da ke aikin samar da zaman lafiya a Mali.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani shirin sanyawa duk wani mutum ko kungiyar da ke zagon kasa ga shirin zaman lafiyar kasar Mali takunkumi.

Takunkumin zai shafi duk wanda ya hana aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2015 da hana kai kayan agaji da cin zarafin Bil Adama da kuma sanya yara kanana cikin yaki.

Daftarin da Faransa ta gabatar ya ce duk wanda aka sanyawa takunkumi za a hana shi tafiye tafiye da rufe kadarorinsa.

Jakadan Faransa a Majalisar Francois Delattre ya ce suna kallon matakin a matsayin wanda zai taimaka wajen samun zaman lafiya a Mali.

Asalin Labari:

RFI Hausa

528total visits,1visits today


Karanta:  An Damke Masu Safarar Mutane a Yammacin Afirka

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.