An Koka Game Da Yawan Cin Bashin Da Gwamnatin Taraba Ke Yi

Yanzu haka dai an soma musayar kalamai a tsakanin yan jam’iyar PDP dake mulkin jihar Taraba, da kuma yan hadakar kungiyar siyasa ta Integrity a jihar game da rancen kudaden da gwamnatin jihar ke karba da kuma yadda gwamnan jihar a yanzu Darius Dickson Isiyaku, ke jagorantar jihar.

A wajen wani taron manema labarai, a Jalingo fadar jihar yan kungiyar sun nuna bacin ransu game da cin bashin gwamnatin jihar, baya ga kudaden tallafin da gwamnatin tarayya ta bada, batun da suka danganta da yunkurin jinginar da jihar Taraba ta hanyar cin bashi.

Hon. Iliyasu Muazu Shagarda, wanda ya taba rike kujerar karamar hukuma a jihar yace son zuciya ne ke jawo wa gwamnatin jihar matsala a yanzu, inda ya bada missali da rashin biyan bukatun ma’aikata da kuma batun bashin da aka karba daga bankin Zenith.

To sai dai a martanin da gwamnatin jihar, kusoshin jam’iyar PDP dake mulkin jihar sun yi fatali da wadannan zarge-zargen da yan hamayya na Integrity group ke yi.

Danladi Sabo- wani kusa ne a PDP yace, Taraba tana samun nasara a yanzu duk kuwa da makudan bashin da gwamnatin Darius ta gada.

Duk kuwa da kokarin da Muryar Amurka ta yi na jin ta bakin kwamishinan yada labaran jihar abin ya ci tura.

To sai dai kuma yayin da ake wannan cece-kuce wanda ke da nasaba batun zaben shekarar 2019, ga masana irinsu Farfesa Muhammad Sani Yahya dake zama tsohon shugaban jami’ar jihar Taraba, TASU, kira yayi ga al’umman jihar da su yi karatun ta natsu a shekarar 2019.

Asalin Labari:

VOA Hausa

5751total visits,1visits today


Karanta:  'Yan jam'iyyar PDP da APC sun ziyarci Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.