An rantsar da Emmerson Mnangagwa sabon shugaban Zimbabwe

An rantsar da Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban kasr Zimbabwe, a wani biki da dumbin jama'a suka taru makil a filin wasa na Harare, babban birnin kasar.

Hakan ya biyo bayan yin murabus da Shugaba Robert Mugabe ya yi ne, bayan shekara 37 da ya shafe yana mulkin ‘kama-karya.’

Korar da Mista Mugabe ya yi wa mataimakin nasa a farkon watan nan ce ta jawo jam’iyya mai mulki ta Zanu-PF da kuma sojoji suka tursasawa Mugabe yin murabus.

Mr Mnangagwa, wanda a baya ya bar kasar, ya koma Zimbabwe daga Afirka Ta Kudu inda ya je neman mafaka.

Jam’iyyar adawa ta nemi Mista Mnangagwa, wanda ya zamto daya daga cikin masu fada a ji a mulkin kasar, da ya kawo karshen al’adar cin-hanci da rashawa da ta addabi kasar.

Yaya ranstuwar shan mulkin ta gudana?

An gabatar da bikin rantsuwar ne a Filin Wasanni na Kasar, kuma masu shirya bikin sun yi kira ga al’ummar Zimbabwe da su fito kwansu da kwarkwatarsu don shaidar wannan rana mai dumbin tarihi.

Mr Mnangagwa ya je wajen ne karkashin rakiyar matarsa Auxilia.

Manyan baki da suka hada da shugabanni daga kasashen Afirka daban-daban sun je bikin rantsuwar.

Babban mai shari’a na kasar Justice Luke Malaba ne ya rantsar da Mr Mnangagwa

Daga bisani kuma an yi ta harba bindiga a matsayin gaisuwar ban girma, sannan kuma sabon shugaban zai gabatar da jawabi.

Asalin Labari:

BBC Hausa

10775total visits,1visits today


Karanta:  Bankuna a Zimbabwe za su fara karbi dabbobi a jingina

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.