An sace gwamman mutane a Kaduna

Rahotanni daga Birnin Gwari a jihar Kaduna a Najeriya na cewa 'yan bindiga sun sace fiye da mutum 80 a kan wata babbar hanya.

Jami’an Kula da Motocin Haya ta NURTW, sun ce an sace mutanan ne a kan wata babbar hanya da ta hada arewaci da kudancin kasar.

Mazauna da jami’an sufuri a yankin Birnin-Gwari sun ce a ranar Lahadi ne ‘yan bindiga suka tsayar da motoci da dama, suka sace dumbin matafiya tare da shigar da su cikin daji, suka kuma bar motocinsu a wajen.

Har yanzu dai ‘yan sanda ba su ce komai ba game da lamarin.

Ana yawan samun matsalar sace mutane don kudin fansa a arewa maso yammacin Najeriya, amma wannan satar ta baya-bayan nan a jihar Kaduna abu ne da bai saba faruwa ba.

Wasu rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun fara tuntubar iyalan mutanen da suka sace din don neman kudin fansa.

A ranar Litinin ne shugaban hafsan soji na Najeriya ya ziyarci yankin domin a kara tsaurara tsaro, sakamakon karuwar hare-hare daga ‘yan bindiga.

‘Yan bindigar sun kashe fiye da mutum 70 a wani kauye a makon da ya gabata.

Najeriya dai na fama kalubalen tsaro da dama. Karuwar satar mutane da ake samu ya zo daidai da ci gaba da kai harin kunar bakin wake da Boko Haram ke yi da kuma rikicin makiyaya da manoma da ke kamari a yankin tsakiyar kasar.

Rashin tsaro dai yana zama wani babban al’amari na siyasa a yayin da kasar ke shirye-shiryen zabe a watan Fabrairun badi, duk da dai gwamnati na cewa tana daukar mataka domin magance su.

Cikin matakan kuwa har da kai sojoji yankunan da ake samun rikce-rkicen.

Kuma tuni Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara.

Karanta:  An Yi Gangamin Ilimantar da Jama'a Kan Illar Ambaliyan Ruwa

Sai dai wasu na ganin zai sha wuya a zaben saboda matsalolin da kasar ke fama da su.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1253total visits,5visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.