An Sami Wani Dan Sanda Kwance A Mace A Kaduna

An sami wani dan sanda wanda har yanzu ba a gane kowanene ba kwance a mace ranar Talata da misalign karfe 5 na safe a dai dai shataletalen kanfanin sayar da motoci na SCOA dake unguwar Shanu cikin jihar Kaduna.

Wakilin kamfani jaridar Daily trust ya rawaito cewa an yiwa dan sandan harbi har guda uku a kirji, ciki dama kafadarsa.

Wasu majiyoyi sun yi zargin cewa dan sanda yayi arangama da ‘yan fashi ne a kan hanyarsa ta dawo gida daga aiki inda ya hadu da ajalinsa.

Wani mazaunin unguwar wanda bai so a ambaci sunansa ba yace “Mun sami gawar ne lokacin da muka fito daga gidajenmu don gudanar da sallar asuba, nan da nan muka shedawa  ‘yan sanda.

“Da yawa na zargin cewa ya hadu da gungun ‘yan fashi ne yayin da suke dawowa daga gurin aika-aikarsu inda suka harbe shi suka kuma gudu da bindigarsa.”

Lokacin da aka tuntubi Kakakin ‘Yan Sandan jihar, ASP Mukhtar Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin

Ya kuma yi alkawarin tuntubar wakilin kamfanin jaridar Daily trust don sheda masa yadda lamarin ya faru amma hakan bai samu ba har lokacin da ake hada wannan rahoton.

Daily trust 6/9/2017

4029total visits,1visits today


Karanta:  Harin Numan: Ba Za Mu Yarda Da Kisan Mummuke Ba – Majalisar Musulmi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.