An sanya James Ibori a kwamitin taron PDP

James Ibori

Jaridar Leadership ta ruwaito cewar an sanya sunan tsohon gwamnan jihar Delta, Cif James Ibori a cikin jerin sunayen wadanda zasu halarci taron babbar jam’iyyar adawa a Najeriya wanda za’ayi a gobe Asabar.

Ibori, wanda ya samu yancin kai a baya bayan nan daga wani daurin shekaru hudu da akayi masa a kasar Birtaniyya ya samu sunan sa a na arba’in da hudu a cikin jerin sunayen.

Taron wanda za’ayi a gobe ana saka ran zai tabbatar da karawa Sanata Ahmed Makarfi tsawon lokacin rikon jam’iyayr ta PDP har izuwa lokacin babban zaben jam’iyyar a watan Nuwanba mai zuwa.

Ibori dai bai taba samun halartar wani taron jam’iyyar ba wanda ta saba kaddamar wa a hedikwatar ta tun bayan dawowar sa Najeriya. Bugu da kari bai samu halartar taron da aka gudanar ba a ranar Laraba data gabata.

Magajinsa a jihar ta Delta, Ifeanyi Okowa ya kasance shugaban kwamitin. Da yake magana akan nadin, tsohon mai taimaka wa Ibori a harkar jarida, Tony Eluemunor, yace nadin yana kan ka’ida sakamakon (Ibori) bai bar jam’iyyar ta PDP ba.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Leadership

752total visits,1visits today


Karanta:  Shin Ya Kamata Buhari Ya Yi wa Gwamnatinsa Garambawul?

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.