‘An yaudari manyan jami’an Donald Trump’

Masu kutse a na’urar Kwamfuta sun yaudari jami’an fadar White House, inda suka yi ta musayar sakwannin email na bogi ba tare da saninsu ba.

Wani sakon email da aka taba aikewa mai bai wa shugaba Trump shawara kan harkokin tsaro na zamani, an yaudare shi ne da sunan surukin shugaban Amurkar Jared Kushner kamar yadda gidan talabijin na CNN ya bayyana.

Shi ma sabon daraktan yada labarai na fadar White House Anthony Scaramucci, an yaudare shi da sunan tsohon shugaban ma’aikatan fadar Reince Priebus.

Ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda masu satar bayanai ke ci gaba da kutse da samun sakwannin email din mutane, a daidai lokacin da ake zargin Rasha ta yi kutse a zaben Amurka da ya gabata.

Sai dai fadar White House ta shaidawa CNN ana gudanar da bincike kan kutse na baya-bayan nan da aka bayyana ta kuma dauki batun da muhimmanci.

Sai dai Prankster ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter inda ya kira kansa da wanda bai yadda da shugabanci ba, tare da yin alkawarin ba zai kara yadawa fadar White House magana ba ko yin shagube.

To amma ya yi gargadin cewa ya kamata a zage damtse don karawa hukumar fasahar sadarwa ta zamani matakan tsaro da cikakkiyar kariya.

Asalin Labari:

BBC Hausa

635total visits,1visits today


Karanta:  An Kafa Dokar Hana Fita a Houston Da Ke Fama Da Ambaliya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.