An Yi Kira Ga Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Matakin Murkushe Boko Haram.

Wannan kiran ya biyo bayan wani sabon vidiyo da Abubakar Shekau ya fitar.

Masana harkokin tsaro suna kira gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauki matakan ba sani ba sabo, wajen tura dakarun kasar cikin dajin Sambisa domin su gama da mayakan sa kai na Boko Haram zama daya.

Baba Yola Mohammed Toungo yayi kiran da gwamnati ta tura illahirin dakarun Najeriya zuwa dajin Sambisa inda za’a yi ta, ta kare. Domin a ganinsa ba hujja bace, cewa yin haka zai rutsa da farar hula, yace yanzu da ba’a dauki wannan mataki ba, farar hulan sun tsira ne?

Da yake magana tunda farko kan sabon fefen vidiyon da shugaban mayakan Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar, Aliko El-Rasheed Haroun, tsohon jami’in leken asirin soja, yace wannan fefen yana nufin cewa kada a dauka cewa an gama da kungiyar tana nan daram, kuna zata ci gaba da gwagwarmayar da take yi na yada akidar ta.

Kan ko wannan wani salo ne na farfaganda, Aliko yace baya jin haka.

Gwamnatin Najeriya dai bata ce uffan ba kan wannan sabon fefen vidiyo da kungiyar ta fitar, da kuma irin barazana da babatu da shugaban ‘yan binidgar yayi ba.

Asalin Labari:

VOA Hausa

644total visits,1visits today


Karanta:  Za A Sabunta Wa’adin Kama Shekau

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.