An Zargi Wani Direba Da Yiwa Agolarsa ‘Yar Shekara 14 Ciki

Wani Direba mai suna Monday Udoh ranar Jumma’a ya bayyana a gaban Babbar Kutun Majistiren Tunubu dake Lagos bisa zargin yiwa ‘yar matarsa mai shekara 14 ciki.

Dan Sanda mai shigar da kara, Sifeto Nurudeen Thomas ya fadawa kotun cewa Udoh mai shekara 39 ya aikata laifin a watan Afirilu a unguwar Eleko Beach dake Ibeju Lekki kusa da Lagos.

Thomas yace wanda ake zargin yayi ta aikata masha’ar da Agolar tasa ne inda daga karshe ya dibga mata ciki.

Yace Udoh wanda ya haifi ‘ya’ya biyu da uwar yarinyar, ya fara aikata masha’ar da karamar yarinyar ne tun shekarar 2014 lokacin da mahaifiyar yarinyar tayi tafiya zuwa kyauyensu.

“Mai girma Alkali, Udoh ya fara yin lalata da yarinyar ne tun tana ‘yar shekara 12 da haihuwa, lokacin da uwar yarinyar tayi tafiya zuwa kyauyensu tabar yarinyar karkashin kulawar mutumin

“Ya kawar mata da budurcinta a watan Afirilu sannan kuma yayi mata ciki. Yanzu haka dai yarinyar na dauke da cikin sama da sati 20.

“Yayi barazanar sawa yarinyar ciwon hauka inda har ta fadawa kowa.

“Amma lokacin da yarinyar ta fahimci tana da ciki, sai ta gudu daga gidan, ta kuma shaidawa daya daga cikin abokan babartata, wadanda su kuma suka shaidawa hukumomin da suka dace.”

Thomas yace wannan laifin ya sabawa sashi na 260 na kundin manyan laifuffukan jihar Lagos na shekarar 2015.

Sashi na 260 ya tanadi daurin shekara 14 a gidan yari ga duk wanda aka kama da irin wannan laifin. Tuni Udoh ya musanta aikata wannan laifin.

Babbar Alkaliyar Kotun Majistirin, Mrs Kikelomo Ayeye, ta saka belin naira miliyan daya kan Udoh. Haka kuma ta ummarci Udoh da ya kawo mutum biyu da zasu iya tsaya masa, haka kuma mutanen dole ne su kasance ma’aikatan gwamnati masu matakin albashi na 15. Ta daga karar zuwa 13 ga watan Satumbar nan da muke ciki don cigaba da sauraran karar. NAN

Karanta:  Fyade: Iyaye na Ficewa Da 'Yayansu a Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira a Maiduguri

Vanguard 8/9/2017

598total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.