Ana kwaso yaran da Boko Haram ta raba da Nigeria

An fara kwaso yaran da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, bayan sun tsere zuwa Jamhuriyar Kamaru, da nufin hada su da iyayensu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu daga cikin yaran dai marayu ne yayin da wasu kuma har yanzu iyayensu na nan da rai kuma an kwaso su ne cikin jirgin sama, wasu daga sansanin ‘yan gudun hijira na Minaoa.

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ce ta dauki gabarar wannan aiki na sada irin wadannan yara da iyaye ko danginsu.

Wakilin BBC, Usman Minjibir ya yi kicibis da yaran da kungiyar ta kwaso a filin jirgin sama na Abuja, bayan sun ci zango a kan hanyar zuwa Maiduguri.

Daya daga cikin yaran wanda ya ce shi dan asalin Bama ne a jihar Borno ya tsere ne sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram, inda ya rabu da iyayensa da su kuma suka nufi Maiduguri a lokacin.

Ya ce ya shafe kimanin shekara biyar rabonsa da ya ga mahaifansa don haka ba shi da tabbacin halin da suke ciki.

A cewarsa ya hada da jami’an kungiyar Red Cross ne a sansanin Minaoa da ke tattara bayanan yara wadanda ba sa tare da iyayensu a can.

Don haka sai shi ma ya bukaci su hada shi da iyayensa wadanda yake da yakini har yanzu suna birnin Maiduguri.

“Ina farin ciki bayan shekara kusan biyar ga shi muna hanyar zuwa Maiduguri. Ina farin ciki,” in ji shi.

Wani rahoto da Majalisar Dinkin duniya ta fitar a shekara ta 2015 ya ce rikicin Boko Haram ya raba kananan yara kimanin miliyan daya da rabi daga gidajen iyayensu.

Boko Haram ba kawai raba kananan yara da iyayensu ta yi, tana ma kuma shigar yaran cikin kungiyar, inda ake sanya su kai hare-hare ciki har da na kunar-bakin-wake.

Karanta:  'Yan gudun hijirar Nigeria na cikin kunci

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross International ta lashi takobin sake sada irin wadannan yara da mahaifansu. kuma a jiya Alhamis ta debo guda takwas.

Ta ce kuma ce za ta ci gaba da wannan aiki har sai ta tabbatar da ganin ta hada fuskokin dukkan wadannan yara da suka tsere suka bar Najeriya.

Asalin Labari:

BBC Hausa

2413total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.