Ana ruguguwar ficewa Florida kafin isowar guguwar Irma

Dubban mutane ne ke ruguguwar ficewa Florida a Amurka kafin isowar mahaukaciyar guguwar Irma da yanzu haka ta isa Cuba dauke da iska mai karfi da ruwan sama.

Guguwar Irma ta isa Cuba bayan ta yi barna a wasu tsibaran yankin Caribbean.

Guguwar da aka ce yanzu ta kai rukuni na biyar na gudu ne a kilomita 190.

Guguwar ta tsallake Bahamas ta fada Cuba.

Amurka ta bukaci mutane Miliyan 6 su kaurace a yayin da guguwar ta doshi Florida.

Akalla mutane 20 suka mutu sakamakon guguwar musamman a tsibiran Caribbean da ta fara yin barna a tsakanin Alhamis zuwa jiya Juma’a.

Asalin Labari:

RFI Hausa

959total visits,4visits today


Karanta:  Saliyo: Za a Yi Wa Daruruwan Gawawwaki Jana'izar Gama-gari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.