Ana Tsare Da Wani Mutum Dan Shekara 29 Bisa Zargin Kisan Dan Sanda A Jihar Nassarawa

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nassarawa ranar Talata sun tabbatar da kama wani mutum dan shekara 29 bisa zargin kisan wani dan sanda mai suna Cpl. Sunday Ayuba a Karamar Hukumar Karu dake cikin Jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Kennedy Idirisu shi ya fadawa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN a garin lafiya cewa wanda ake zargin ya doki dan sandan yayin da dan sandan ke kokarin kama shi bisa laifin da ya shafi damfara.

Idirisu yace bincike ya nuna cewa an zirgi wasu gungun ‘yan damfara da damfarar wata mata mai suna Esther Amos kudi kimanin Naira Miliyan uku inda wanda ake zargin (wanda ba a bayyana sunansa ba) yayi nufi tamaikawa matar kudinta su fito.

“Wanda ake zargin yayi nufin taimakawa matar, inda ita kuma Esther ta yarda zata biya shi kudi N200,000.

“Esther da wanda ake zargin suka shirya ta wayar tarho cewa zasu hadu a daidai mahadar nan ta Ado a Karamar Hukumar Karu a wannan rana don cika alkawarin yadda kudin matar zasu fito.

“Ba tare da sanin wanda ake zargin ba, Esther ta tuntubi ‘yan sanda, haka kuma caji ofis din ‘yan sanda na Mararaba sun hada matar da marigayi Cpl. Ayuba inda ya jirasu a daidai gurin da sukayi alkawarin da nufin kama wanda ake zargin.

“Da zuwansu gurin sai Esther ta kira nambar wayar wanda ake zargin, daga ganinsa shi kuma marigayi sai ya zaburo don kama shi.

“Ana haka ne shi kuma wanda ake zargin ya doki dan sandan ya kuma kama gudu, amma daga bisani masu zirga-zirga a gurin sun kamo shi suka kuma mikawa ‘yan sanda shi a take,” a cewarsa.

Karanta:  Adamawa: Boko Haram Ta Kone Garin Yumbuli Kurmus

Idirisu ya kara da cewa an dauki dan sandan an kai shi asibiti, inda daga baya kuma ya rasa ransa.

A cewar kakakin ‘yan sandan,za a caji wanda ake zargin kamar yadda doka ta nuna.

“Dama can zargin damfarar da wanda ake zargin sunansa ya fito tuni yana gaban kotu a Abuja,” in ji shi.

Tunda fari dai wanda ake zargin yayi ikirarin cewa shi injiniya ne mai digiri a fannin lantarki daga Jami’ar Fasaha dake Owerri wato FUTO, ya kuma shaidawa kamfanin Dillancin Labarai na NAN cewa ba nufin kashe dan sandan yayi ba, yayi yinkurin kare kansa ne.

A cewar wanda ake zargin, a watan Mayu ne ya kammala bautar kasa wato NYSC a Jihar Nassarawa

“Banyi nufin cutar da dan sandan ba, abinda nayi kokarin yi shi ne kawai na kare kaina.

“Banma san shi dan sanda bane. Nayi kokarin tseratar da kaina ne daga kamunsa, sai na kuskure nayi masa gula shi kuma ya fadi,” a cewarsa.

Bisa zargin damfarar kuma, wanda ake zargin cewa yayi ya sami wayar Esther ne ta shafinta na dandalin sada zumunta na facebook inda ya tsinkayi sirikinsa na magana game da kudin Naira miliyan uku shi kuma yayi nufin taimaka mata kudin nata su fito.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

251total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.