Ana Zaman Dar-dar a Yankin Madagali Sanadiyar Sabon Harin Boko Haram

Tun daga yammacin jiya ne mayakan Boko Haram dauke da muggan makamai suka farma kauyen Bakin Dutse cikin karamar hukumar Madagali, a jihar Adamawa kuma kawo yanzu ba’a tantance adadin mutanen da wannan sabon harin ya rutsa dasu ba.

Kamar yadda wasu da suka tsallake rijiya da baya suka bayyana, mayakan na Boko Haram dauke da muggan makamai, sun soma kai farmaki ne daga yankin Bakin Dutse dake kusa da garin Gulak hedikwatar karamar hukumar suna harbe-harbe ba kakkautawa inda aka dauki dogon lokaci ana dauki ba dadi a tsakaninsu da sojoji da kuma yan yakin sa kai na maharba da yan banga.

Mazauna yankin da ke boye sun bayyana cewa ya zuwa yanzu ba’a san adadin wadanda harin ya shafa ba.

Shima da yake tabbatar da wannan hari da aka kai cikin dare, gwamnan jihar Adamawa Senata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla ya ce , an tura karin sojoji, yayin da ya bukaci al’ummomin yankin Madagali da Michika da su kwantar da hankulansu.

Shugabanin yankin su ma sun nuna damuwrasu da irin wadannan sabbin hare haren da mayakan na Boko Haram ke kaiwa a yanzu kamar yadda Hon.Yusuf Muhammad shugaban karamar hukumar Madagali yayi tsokaci.

Ya zuwa yanzu hukumomin tsaro basu yi karin haske ba tukunna dangane da wadannan sabbin hare haren da aka kai, yayin da jama’a ke cikin zaman dar-dar.

Asalin Labari:

VOA Hausa

4531total visits,2visits today


Karanta:  Dubban 'yan jam'iyar APC sun cika da buri

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.