Ana Zargin Sojoji da Cin Zarafin Jama’a a Naurar Banki ta ATM a Yola

Farar hula dake mu’amala da bankunan kasuwanci a Yola fadar jihar Adamawa suna kokawa da abinda suka kira cin fuska da cin mutunci da kananan jami’an soja ke yi masu a injunan bankuna na cire kudi ko ATM dake harabobin bankuna.

Wakilin Sashen Hausa ya ci karo da irin wannan lamarin a daya daga cikin bankunan kasuwanci inda hatsaniya ta kaure tsakanin wata matar aure goye da jariri da kuma yaro dan kasa da shekara shida da wani karamin jami’in soja da ya ki bin layi duk da cewa ya tarar da wasu mutane a layi da suka share sa’o’i suna jiran nasu zagaye na cire kudi da ta bukaci shi wannan jami’in sojan ya bi layi daidai da tsarin da bankunan suka shinfida.

Sakamakon bincike da Murya Amurka ta gudanar a hirarraki da ta yi da jama’a ya nuna a wasu lokutan idan takaddamar ta kazanta ta kan kai ga raunata farar hula kamar yadda Malam Adamu Ali wanda ya shaida shi ma ya sha da kyar a wata cacar baki da wani jami’in soja da yaki bin layi a wani bankin dake a garin Yola.

Hukumomin rundunar soja dake Yola inji ta bakin jami’in hulda da jama’a Kaften Adamu Ngulde babu wani rahoto na musgunawa ko cin mutunci da zarafi da aka kai ofishinsa kan wannan batun. A iya saninsa inji jami’in jami’ansu na yin da’a ga doka da oda.

Ya kare zargin da ake yi wa jami’an soja na karbar na goro, dalili ma da ya sa suke rike katuna fiye da daya don cirewa jama’a kudi musamman lokutan da aka yi albashin ma’aikata. Kaften Adamu Ngulde ya musanta hakan na abkuwa. Ya ce katunan na wasu jami’ansu ne dake yankunan da suke yaki da Boko Haram da babu bankuna.

Wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Hussaini Hammangabdo ya ce akwai abin dubawa game da korafin jama’a da ya kamata hukumomin soja su yi la’akari da shi kafin hakurin farar hular ya kai ga kurewa.

Karanta:  Wasu 'Yanbindiga Sun Yiwa Mutane Yankan Rago a Midul, Adamawa

Kokarin jin ta bakin jami’an bankunan dake Yola ya cutura domin sun haikance sai sun samu izini daga hekwatarsu dake Abuja.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1089total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.