Ana Zargin Wani Dan Sanda Da Kashe Kansa Saboda Sauya Masa Gurin Aiki Zuwa Maiduguri, ‘Yan Sanda Sun Karyata Zargin

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ebonyi sun karyata labarin dake kewayawa garin Abakaliki cewa daya daga cikin ‘yan sandan jihar ya kashe kansa ranar Litinin saboda sauya masa gurin aiki zuwa Maiduguri.

ASP. Loveth Odah, Maimagana da Yawun ‘Yan Sandan Jihar ya fadawa manema labarai ranar Talata cewa Oyibe bai kashe kansa da gangan ba  kamar yadda ake yadawa a gari.

“Da gaske ne Oyibe na cikin wadanda aka canza musu gurin aiki zuwa Maiduguri, amma hakan bai sashi kashe kansa ba saboda kwararren dan sanda ne.

“Ya fadawa ‘yarsa cewa zai je ya debo ruwa a rijiya, amma abin rashin jin dadi jim kadan da tafiyarsa sai aka sameshi a cikin rijiyar.

“Zai iya yiyuwa cewa tsautsayi ne yasa shi fadawa rijiyar yayin debo ruwan ko kuma wani ne ya turashi cikin rijiyar da gangan, a fadarsa.

Odah yace bincike yayi nisa kan lamarin sannan kuma rundunar zata bayyana dalilin afkuwar lamarin

“Wannan ba shi ne karo na farko da aka samu wani ya fada rijiya ba, shi yasa ni mamakin yadda mutane ke kirkirar fassarori da dama kan wannan lamarin da ya shafi dan sanda.

“Mutuwar dan sanda musamman a wannan yanayin ba abun murna bane, shi yasa zamu fayyace gaskiyar lamarin,” a cewarsa

Wani abokin mamacin da ya zanta da ‘yan jarida wanda bai so a ambaci sunansa ba yayi bayanin cewa Oyibe yayi ta korafi ga abokansa kan sauyin gurin aikin zuwa Maiduguri.

“Ya bayyana kaduwarsa mutuka kan aiki a Maiduguri, haka kuma yana tunanin makomar yaransa musamman yadda matarsa ta riga mu gidan gasgiya shekaru kadan da suka wuce.

Karanta:  Kungiyar Malaman jami’a tace Sojoji Sun Shara Karya.

“Mutum ne mai son zaman lafiya wanda marayun ‘ya’yansa da ‘yan uwa da abokan arziki zasuyi mutukar rashinsa, a cewarsa.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

529total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.