Asusun Bai Daya: NULGE Na Zargin Gwamnoni Da Babakere

Yayin da takaddamar da ake yi kan batun asusun bai daya tsakanin kanananan hukumomi da gwamnatocin jahohi da kuma batun babakere a batutuwa dabandaban da ake zargin gwamnonin jahohi da yi, a yanzu kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta shiga yin zanga-zanga.

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa ta zargi gwamnonin jihohi da kin sakarwa kananan hukumomi mara wajen sarrafa kaso da suke amsa daga asusun gwamnatin tarayya, kin gudanar da sahihiyar zabe na kananan hukumomi da tauye masu hakki a matsayin masalolin da suke gurgunta harkokin gudanarwarsu.

Wannan bayanin na kunshe cikin takardar da shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Najeriya Komrad Ibrahim khalil ya gabatawa kakakin majalisar dokoki ta jihar Adamawa, wanda mataimakin sa Hon. Sunday Peters ya wakilta a ci gaba da gangamin fafatukar neman samun yancin cin gashin kai a gyarar kundin tsarin mulkin kasa da tuni majalisun tarayya suka amince da ita.

Komrad Ibrahim Khalil ya ce matukar aka cigaba da bin tsarin da ake bi yanzu, kananan hukumomi da mazauna karkara zasu ci gaba da kasancewa cikin talauci da rashin anfana da muhimman abubuwan more rayuwa wadanda su ne ke haifar da rashin tsaro da kuma yawan kaura daga karkara zuwa birane.

Na yi hira da mataimakin kakakin majalisar dakokin jihar Adamawa Hon. Sunday Peters kan fa’idar wannan gwagwarmaya ta nemar cin gashin kai, wanda ya bayyana bukatar kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi da suka gabatar wa majalisar tamkar sara ce kan gaba a dai dai dalokacin da su ma majalisun dokokin jihohi ke neman tasu ‘yancin cin gashin kai daga gwamnonin jihohi.

Ya ce ya yi imanin samar wa bangarorin gwamnati ‘yancin cin gashin kai zai samar da wata dama ta aiwatar da ayyukansu ba tare da takura ba, kamar yadda tsarin yake yanzu da gwamnonin jihohi ke amfani da karfi fiye da kima na su ne wuka su ne nama.

Karanta:  Adamawa: Boko Haram Ta Kone Garin Yumbuli Kurmus

Wasu daga cikin kwalayen da ‘ya’yan kungiyar ma’aikatan ke dauke da su na dauke da sakonni na kashedi ga wakilan majalisun dokokin na ‘ko su amince da gyarar dokar tsarin gudanar da kananan hukumomi ko mu sauya ku a zaben 2019’ da’ kuma mu na Magana da yawun mazauna karkara da tsarin da ake amfani da shi yanzu ba ya tsinana wa komai’.

Asalin Labari:

VOA Hausa

546total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.