ASUU ta fara yajin aikin sai baba ta gani a Nigeria

Kungiyar malaman jami'oin na Najeriya (ASUU) sun shiga yajin aiki, inda malamai suka dakatar da koyarwa da sauran ayyukan da suka shafi karatu a daukacin jami'oin gwamnatin tarayya da ke kasar.

Kungiyar ta ce ta shiga yajin aikin ne wanda ya fara aiki a ranar Lahadi saboda rashin aiwatar da yarjejniyar da ta cimma da gwamnatin a shekarar 2009.

Cikin batutuwan da kungiyar ke korafi a kai sun hada da rashin zuba isassun kudade a jami’oi da rashin biyan malamai cikakken albashi da rashin biyansu ragowar kashi 60 cikin dari na kudaden alawus-alwasu dinsu, wanda kungiyar ta ce duka an cimma yarjejeniya a kansu.

Batun kafa kamfani mai zaman kansa da zai dinga kula da harkar fanshon ‘ya’yan kungiyar na daga ciki batutuwan da kungiyar ta ce gwamnatin ta gaza aiwatarwa, kamar yadda Dr. Nasir Isa Fagge shi ne tsohon shugaban kungiyar malaman ya bayyana a lokacin taron.

Ya kara da cewa a watan Nowambar shekarar 2016 kungiyar ta shiga yajin aikin gargadi na mako guda, domin matsin lamba ga gwamnati wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar da kungiyar ta cimma tare da gwamnatin Najeriyar tun a shekarar 2009, amma hakarsu bata cimma ruwa ba.

A cikin bukatun da kungiyar ASUUn ta gabatar, har da kira ga gwamnati ta tabbatar da an sako wasu malaman jam’ar Maiduguri da kungiyar Boko Haram ta ke garkuwa da su.

Wannan batu na yajin aikin ya ja hankalin ma’abota shafukan sada zumunta, inda suka yi ta tafka mahawara game da dalilai da tasirin wannan matakin.

Mista Ogunyemi ya ce yajin aikin zai shafi dukkan jami’o’in gwamnatin Najeriya dake ko ina a fadin kasar.

“A lokacin wannan yajin aikin, zamu daina koyarwa, kuma babu shirya jarabawa da halartar tarurruka a dukkan rassanmu”, inji shi.

Kawo yanzu gwamnati ba ta kai ga cewa komai ba game da yajin aikin, sai dai tuni dalibai da iyayen yara suka fara nuna fargaba a kan tasirin da yajin aikin zai yi a harkar karatun dalibai. A ‘yan shekarun baya dai kungiyar ta ASUU ta shiga yaje-yajen aiki, lamarin da wasu ke ganin ya taimaka wajen gurgunta harkar karatu a jami’oin.

Asalin Labari:

BBC Hausa

414total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.