Ba ma goyon bayan raba Najeriya – Sheikh Dahiru Bauchi

A ranar Asabar da ta gabata ce mabiya Darikar Tijjaniyya suka yi wani babban taro a Bauchi a karkashin jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda shehunnai da halifofi da jagororin darikar daga jihohin Najeriya suka halarta da nufin bunkasa harkar ilimi da hadin kan mabiyar darikar, kuma aka yanke shawarar kafa Majalisar Koli ta Malaman Darikar Tijjaniyya a Najeriya. A karshen taron Sheikh Dahiru Bauchi ya amsa tambayoyin manema labarai kamar haka:

Allah gafarta ko za ka fada mana dalilin wannan taro?

Dalilin wannan taro nun kira ’yan uwanmu ’yan Tijjaniyya na Najeriya ne mu tattauna halin da muke ciki da yadda za mu shirya mafita daga matsalar da muke ciki. Babban abu dai muna kira ne don mu hada kanmu, da ma mu jama’a ce guda daya, jama’ar Musulunci, jama’ar Darikar Tijjaniyya, jama’an Faydar Shehu Ibrahim. Haduwar tamu mun tunatar da mutanen da suke kallonmu cewa duk Najeriya babu jama’a da suke hadaddiyar jama’a mai murya daya mai mafuskanta daya kamar mu ’yan Tijjaniyya. Saboda haka mu san haka mu hada kanmu mu yi karfi domin mu yi maganin abubuwan da suke damunmu a Najeriya. Babban abin da yake damunmu a Najeriya duk da cewa  mu ne jama’a da kanmu a hade yake, muryar daya, mafuskantar mu daya amma da yake sha’aninmu ya saba da sha’anin siyasa, ka san ’yan siyasa su yawan jama’a ake nema ba yawan jama’ar gaskiya ba, saboda haka sai ya zamo komai namu sai a mai da mu baya a ture mu kamar mu ba ’yan kasa ba. Wadansu da su ba komai ba cikin ilimin addini ko ma ba su da ilimin addinin gaba daya a jawo su a ce su ne, a ce su ne jagorori kuma dole a tursasa mutane ya zama suna bayansu. A taron mun yi maganar wannan, kuma mu ’yan Tijjaniyya za mu hada kanmu mu yi maganin abubuwan da suke damunmu ta hanyar ruwan sanyi ba ta hanyar tayar da hankalin jama’a ba, don dama mu ba a san mu da ta da hankali ba.

A kwanan baya Gwamnatin Tarayya ta nemi ta taimaka wa makarantun allo da na Islamiyya da na koyar da Alkur’ani me Shehi zai ce kan haka?

Ai mu a hade muke kuma gwamnatin tana ganinmu a hade din, ita za mu tambaya mene ne dalili tana ganinmu a hade kuma tana neman jama’a amma aka mai da mu a baya? Kuma in tsangayoyin ne ma mun fi kowa tsangayoyi, masu karatun Alkur’ani babu jama’ar da suke fitar da sama da mutum dubu kowace shekara sababbin mahaddata kamar mu ’yan Tijjaniyya, ai sun san mu.

Wato kun dauki kamar matakin daidaita al’amura ne don ku nuna wa gwamnati bukatunku da yadda kuke ganin za a daidata al’amura?

Eh, abin da muka sa a gaba ke nan, mu nuna wa mutane kanmu a hade yake, mu nuna wa gwamnati kanmu a hade yake, in tana neman taimaka wa wadansu mutane masu kama da mu, to ga mu ta taimaka din.

Karanta:  Gwamna El-Rufai ya samar da sabbin kayan aiki a babban asibitin Kafanchan

Sau da yawa ana batun almajiranci wadansu su ce yaya za a kawar da shi a Najeriya, me za ka ce dangane da haka ?

Al’amarin almajiranci wadansu mutane ne batagari suke shiga cikin almajirai su nuna kamar su almajirai ne suna yin miyagun abubuwa. Amma almajiranci ai yana da asali, ma’ana almuhajir mutumin da ya yi hijira, ya kaurato ya bar garinsu ya koma garin Annabi shi ne ake kiransa almuhajir, to su ne almajirai din har ma munafukan Madina suka ce ya kamata a hada kai a hana musu abinci su mutanen Annabi din, saboda haka almajiranci abu ne mai asali dukan Musulmi ai almajiri ne tunda ya soma da karatun Alkurani kafin ya shiga wani abu.

Wane sako Shehi ke da shi ga al’ummar Musulmi da kuma gwamnati?

Sakonmu ga dukan Musulmi mu hada kanmu mu zama abu daya, sannan musamman mu da muke ’yan Tijjaniyya mu sake hada kanmu a cikin Musulunci din, mu sake zamowa wani abu daban, mu hada kai don mu samu mu cimma burinmu wajen koyar da yaranmu ilimin addini na gaskiya na soyayyar Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), kuma mu nuna wa mutane kamar yadda suka sanmu mu mutane ne masu son zama lafiya, kuma mu gaya wa Najeriya gaba daya. Maganar cewa za a yanke Najeriya a yi wata kasa Biyafara ba ruwanmu da wannan. Muna gaya wa gwamnati mutanen da suke cewa a kori Ibo daga Arewa su koma kasarsu ba ruwanmu da wannan. Mu Najeriya daya muka sani kuma a cikinta muke rayuwa, duk mai goyon bayan Najeriya a matsayin hadaddiya muna tare da shi, amma ba ma goyon bayan wanda ya ce a raba Najeriya ko a kori wadansu daga Arewa.

Karanta:  Boko Haram ta kashe sojojin Nigeria tara a Borno

Wace matsaya kuka cimma a karshen taron?

Matsayar da muka cimma kamar yadda kwamitin da suka tace aka ba da sanarwar bayan taro a karkashin jagorancin Farfesa Abdullahi Okene da Sakataren Kwamitin Nasiru Madaki, kuma Injiniya Salisu Shehu Maihula ya gabatar a karshen taron batutuwa ne guda 17 aka cimma matsaya cewa shehunnai da halifofi da mukaddaman Darikar Tijjaniyya su wayar da kan al’ummansu ta hanyar da za a inganta makarantun Alku’rani da na Islamiyya yadda za su dace da zamani, ta hanyar sanar da alkaluma da cikakkun bayanai kan makarantun. Kuma an amince za a mika wadannan alkaluma da bayanan makarantun zuwa hannun Mu’assasar Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Sannan an ja hankalin jama’a game da muhimmancin yin amfani da kafofin watsa labarai wajen yada manufofinmu tare da kafa wasu kafofin watsa labarai masu zaman kansu. An bai wa gwamnati shawara ta kafa hukumar da za ta kula da makarantun Alkur’ani in za ta nada wa hukumar shugabanni ta nada wadanda suke da alaka da makarantun. Kuma an bukaci gwamnati ta taimaka wa makarantun Alkur’ani da na Islamiyya a kan manhajar da suka yarda da ita. Kuma a wajen taron mun lura cewa iyayen yara suna kaurace wa makarantun firamare da sakandare na gwamnati ne saboda rashin gamsuwa da manhajar da ake koyarwa da suka shafi karatun addini. Kuma mun jawo hankalin mahalarta cewa su raya al’adun magabatanmu ta hanyar ziyarce-ziyarcen juna don karfafa dankon zumunci. Kuma mun jan hankalin al’ummar duniya musamman kafofin wata labarai su san cewa darika ba kungiya ba ce, hanya ce ta neman karin kusaci ga Allah Ubangijin dukkan halitta, don haka a daina kiran darikun waliyyai a matsayin kungiya. Kuma mun amince za a kafa Majalisa Koli ta Malaman Darikar Tijjaniyya wacce za ta jagoranci al’amuran addini, tare da fuskantar matsaloli masu tasowa da murya daya. Sannan za a samar da wani tsari da zai taimaka wa zawiyyoyi domin samun hanyar dogaro da kai ta hanyar inganta tattalin arzikinmu domin ciyar da Darikar Tijjaniyya da Failar Shehu Ibrahim Radiyallanu Anhu gaba.

Karanta:  An Yi Gangamin Ilimantar da Jama'a Kan Illar Ambaliyan Ruwa

Kuma taron ya yaba wa gwamnati bisa matakan da take dauka ta fuskar tsaro da yaki da cin hanci da rashawa, tare da jan hankali a rika yin adalci da kiyaye hakkin dan Adam, kamar yadda muka fada a baya. Taron ba ya goyon bayan masu kiran a raba Najeriya ko a kori wadansu jinsi daga Arewa. Taron ya yi kira a karfafa hadin kan ’yan kasa da son juna da kaunar juna. Haka kuma ko kadan ba mu yarda da dokokin da suka saba wa shari’ar Musulunci da wadansu ke son kafawa ba, kamar hana iyaye su aurar da ’ya’yansu mata ’yan kasa da shekara 18 ba, da kuma dokar da ake nema a ba da iko wa yaro ya kai karar iyayensa, domin kowane yaro yana karkashin kulawar mahaifansa ne har ya balaga. Mun sake shawartar gwamnati kan gyaran tattalin arzikin kasa don a sauwaka wa jama’a halin da suke ciki na matsuwa da talauci da wahalhalun rayuwa. Mun kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta sassauta wa Musulmi wajen biyan kudin aikin Hajji domin sauke faralin da Allah Ya dora musu, kuma ta kara tsaurara matakan tsaro wajen yaki da masu garkuwa da mutane da yi wa kananan yara fyade. A karshe mun yi  addu’oi na musamman domin samun dauwamammen zaman lafiya a kasarmu Najeriya tare da yin addu’a ga Shugaban Kasa da fatan Allah Ya ba shi lafiya, ya dawo da shi gida lafiya ya ci gaba da yin ayyukansa.

 

Asalin Labari:

Aminiya

1958total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.