Ba Zamu Lamunci Yunkurin Raba Kan Kasa Ba – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin murkushe yan ta'adda da masu neman raba kan al’ummar kasar.

A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar, shugaban yace ba zasu bari masu fakewa da kabilanci da siyasa su samu damar raba kan yan Najeriya ba.

Bayan sakon godiya ga ‘yan Najeriya, shugaban ya bayyana farin cikin sa na komawa gida, inda yace lokacin zaman sa a London yayi ta bibiyan abubuwan dake faruwa a Najeriya, musamman yadda wasu sukayi ta amfani da kafar sadarwa domin neman raba kan kasar.

Buhari yace lokacin da ya yanke hukuncin shigasiyasa a shekarar 2003, tsohon shugaban Yan Tawayen Najeriya, Odumegwu Ojukwu ya ziyarce shi a garin su dake Daura, inda suka kwashe kwanaki biyu suna tattaunawa kan matsalolin Najeriya, kana suka yanke hukuncin cewar babu abinda zai raba kan kasar.

Shugaban yace ba zasu bari wasu bata gari suyi amfani da yan matsalolin da ake da su a kasa wajen neman raba ta ba, kana da zaran an samu matsala su tsallake su bar kasar.

Buhari yace kowanne dan Najeriya na da damar zama a duk inda yake so ba tare da tsangwama ba, kuma idan wasu jama’a na da korafi, suna iy aamfani da Majalisar dokoki ko kuma Majalisar koli domin gabatar da su.

Shugaban ya bukaci jami’an tsaro su murkushe yan ta’adda da masu aikata laifufuka domin a samu zaman lafiya, inda ya sha alwashin magance book haram da masu garkuwa da mutane da rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Asalin Labari:

RFI Hausa

576total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.