Babu Fasfo ga wanda bashi da katin dan kasa

Gwamnatin Tarayya ta ce duk wanda bashi da lambar dan Kasa kafin shekara ta 2018 ba zai samu Fasfo ba

Gwamnatin tarayya ta ce daga daya ga watan Janairun shekara ta 2018 duk wani dan Najeriya da ba yi da lambar tantance dan kasa ba za a yi masa fasfon tafiye-tafiye ba.

Haka zalika ta ce duk wani dan kasar nan da ke zaune a kasashen ketare wanda kuma yake bukatar sabon fasfo ko sabuntawa ya zama wajibi ya fara samun lamba daga hukumar rajistan ‘yan kasa.

Kwanturola Janar na hukumar shige da fice ta kasa Muhammed Babandede ne ya bayyana haka jiya a Abuja, yayin wani taron masu ruwa da tsaki.

Ya ce an yi hakan ne kuwa domin saukaka hanyoyin gudanar da kasuwanci a kasar nan.

Muhammed Babandede ya ce babban kalubale da ke addabar kasar nan a yanzu shi ne rashin tantance adadin mutanen da ke zuba jarinsu wanda a dalilin haka ya sanya kamfanoni da ‘yan kasuwa basa samun damar musayar fasaha da suke dashi.

Tun da farko da ya ke gabatar da nasa jawabin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan fasahar sadarwa, Lanre Osibona, ya ce lambar tantance dan kasar zai taimaka wajen dakile rashin tsaro da ke addabar kasar nan ba ya ga taimakawa wajen saukaka gudanar da kasuwanci.

Asalin Labari:

Freedom Radio

779total visits,1visits today


Karanta:  Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.