Babu inda ‘yan kabilar Igbo zasuje – Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa babu inda ‘yan kabilar Igbo mazauna birnin na Kano zasuje a sakamakon wa’adi da kungiyar matasan Arewa ta basu.

Gamna Ganduje ya bayyana hakan ne a jiya Asabar 5 ga watan Augusta a yayin wata ziyara da ‘yan kungiyar Ibgo suka kai masa inda yake cewa manyan Arewa, ‘yan siyasa da masu fada aji sun jawa samarin kunne sakamakon furucin su na korar ‘yan kabilar ta Igbo daga yankin. Ganduje yayi nuni da cewa babu wata kabila da zata fice daga garin Kano.

“Gwamnonin Arewa ba zasu bayar da goyon baya ba na tayar da zaune tsaye, sannan kabilar a jihar Igbo suna nan tare damu har abada” inji Ganduje. Ya ci gaba da cewa “Ko da kuna so ku tafi akan kanku, to ba zamu barku ba. Nan shine gidan ku”.

“Al’umma ‘yan kasashen waje kan su suna zama cikin kwanciyar hankali a garin Kano kuma suna hulda mai mana’a, don haka babu wani dalili na razana yan kasar mu Najeriya.”

“Abinda yake faruwa a kasar Sudan darasi ne a gare mu. Rabuwar kasar su babu inda ya kaisu. Don haka ba zamu amince da irin wannan tsautsayin ba”

A jawabinsa, shugaban kungiyar Igbo  Cif Chi Nwogu yace sunzo garin na Kano ne domin ganawa da matasan Arewa sakamakon wa’adin tashi da kungiyar ta bawa ‘yan kabilar Igbo.

783total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.