Bama Bukatar Wani Sabon Yakin – Ohanaeze Ndigbo

Shugaban Kungiyar Igbo Zalla wato Ohanaeze Ndigbo na Kasa,  Mr. John Nwodo, yayi kira ga ‘yan Nigeriya daga kowacce kabila, addini ko nahiya da su zauna lafiya. Inda yake cewa kasar bata bukatar shiga wani yaki daban.

Mr Nwodo yayi wannan maganar ne a Gombe yayin da ya jagoranci shugabannin kabilar Igbo na daukacin arewacin kasar da babban birnin tarayya ziyarar girmamawa gurin Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo.

Ya yi gargadin cewa halin da ke faruwa a cikin kasar yayi kamanceceniya da abin da ya faru a cikin shekarun 1960 lokacin da kasar ta fuskanci yakin basasa wanda yayi sanadiyar mutuwar sama da mutane miliyan uku

Yace mutane kamar shi wadanda suka sheda yakin Biafra bazasu kyale barkewar wani rikicin ba wanda zai jefa kasar cikin wani bala’in.

A cewarsa kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yarda da manufar ziyarar ‘yan arewa tun kafin shawarar da gwamnoni 19 na arewacin kasar suka yanke na ziyarar kudu masu gabashin kasar.

“Gwamnonin sun ziyarce mu, yanzu kuma muma gamu anan, wannan shi ke nuna cewa jirgi daya ne ya kwaso mu duka kuma abu daya muke mafarki,” a ta bakinsa.

Ya tabbatarwa wadanda ba ‘yan kabilar Igbo ba mazauna yankin kudu masu gabashin kasar ingantanciyar kariya, yana mai isar da matakin gwamnonin yankin na tsare lafiyarsu.

“Gwamnoninmu na cewa duk wani dan kabilar Igbo dake son kashe dan arewa, kamata yayi yazo ya fara ta kansu. Kamar yadda nake shugaban kungiyar Igbo, nima ina cewa kamata yayi wannan mutumin ya fara kashe ni,” a cewar Mr. Nwodo.

Shugaban kungiyar ta Ohanaeze Ndigbo ya bayyana cewa kiraye-kirayen raba kasar da ake fuskanta yanzu wani yinkuri ne na makiya Nijeriya wanda ke bakin cikin ni’imomin da Allah yayiwa kasar.

Karanta:  Iyaye na ba da 'ya'yansu ga Boko Haram – Sojin Nigeria

Ya roki gwamna Dankwambo da ya isar da sakon zaman lafiyar da shugabanin Igbo ke dauke da shi zuwa ga jama’ar jihar dama gabadayan yankin arewa masu gabashin kasar.

Yayin da yake maida jawabi, Matemakin Gwamnan Jihar, Mr. Charles Iliya wanda ya wakilci gwamna Dankwambo tabbatarwa yayi cewa jihar gida ne ga kowa, ya kara da cewa shirye-shirye sunyi nisa na samar da zaman lafiya a jihar.

Yayi bayanin cewa, anyi wata ganawa ta musamman da ‘yan siyasa, shugabanin gargajiya dana addinai a jihar don samun hadin kan kasa.

“Tuni muka mika sako ga jama’ar jihar cewa kada su zauna cikin nuna kyama da yada jita-jita,” a cewarsa.

Ya bayyana sauran kabilu mazauna Gombe a matsayin ‘yan asalin jihar wanda ake bukatar gudunmowarsu don karin cigaban jihar.  Mr. Nwodo da tawagarsa sun kuma gana da al’ummar Igbo mazauna jihar.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

1832total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.