Ban Damu Da Rashin Tabbatar Da Ni Ba – Ibrahim Magu

Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa shi sam rashin tabbatar da shi a matsayin Shugaban Hukumar da majalisar dattawa ta ki yi bai dame shi ba, kuma ba zai taba damunsa ba, kuma kullum wannan abin da ke faruwa sai kara masa kaimi yake yi wajen ci gaba da bayar da tasa gudumawar wajen kawo karshen cin hanci da rashawa da sace dukiyar jama’a da ake yi a kasar nan.

Malam Ibrahim Magu ya furta wadannan kalamai ne a cikin jawabinsa a wata ziyara ta musamman  da ya kawo babban ofishin LEADERSHIP da ke Abuja jiya Talata, wanda Shugaban kamfanin, Sam Nda-Isaiah tare da sauran manyan kamfanin suka tarbe shi.

Shugaban na EFCC ya ci gaba da cewa shi dama yaki da miyagun halaye abubuwa ne da dole sai an bi su a hankali, domin su masu aikatawa ba za su bari abubuwa su tafi a cikin dadi ba. Ya ce duk wadannan abubyuwa da suke faruwa tsakaninsa da majalisar, sakamakon yaki ne da rashawar, domin haka shi abin ma kara masa kaimi yake yi a akan abin da ya sa a gaba, tun ya samu gwamnatin da daukar wa kanta kawar da wannan mummunar dabi’a.

Inda tun a jawabin nasa ya bayyana wa masu masaukinbnasa cewa ya kawo wannan ziyara ce domin nuna godiyarsa bisa irin goyon bayan da wannana kafar yada labarai ta LEADERSHIP ke ba shi, tare da Hukumarsa wajen ganin nasarar wannan yaki da yake yi. Wanda kuma ya y i fatan za a ci gaba da ba Hukumar irin wannan gudumawa har haka ta cimma ruwa.

Cikin jawabinsa na maraba, Sam Nda-Isaiah ya nuna matukar farin cikinsa da wannan ziyara, wanda ya ce dama shi Magu ba bakon wannan kamfani ba ne, don haka ne ma kamfanin ya ba shi lambar yabo bisa kokarinsa wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Karanta:  EFCC ta kwato 'naira biliyan 329 daga kamfanonin mai'
Asalin Labari:

LEADERSHIP Hausa

593total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.