Ban koma PDP ba – Rabiu Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar APC ya karyata rahotannin cewar ya bar jam’iyyar ta sa izuwa PDP.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewar a jiya kafafan sada zumunta sun yada labarin cewar Sanata Kwankwaso ya fita daga APC zuwa PDP tare da ‘yan majalisu 10 na majalisar wakilai ta kasa.

Kwankwaso ya musanta hakan ne ta hanyar maitaimaka masa na musamman, Nafiu Umar Dankura, inda yake cewa yana nan daram a APC.

“Ina so na tabbatar cewar wannan jita jita ce wacce bata da tushe. Jita jita ce kawai da take yawo a cikin shafukan sada zumunta kan cewar maigirma Sanata ya fita daga APC zuwa PDP. Ba gaskiya bane kamar yadda kowa ya sani cewar Sanata yana daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC. Muna jin dadin yadda shugabancin jam’iyya yake tafiya.” Inji Dankura.

Dankura ya kara da cewa Kwankwaso yana jin dadin zamansa a APC.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

2127total visits,1visits today


Karanta:  'Masu fuska biyu a gwamnatin Buhari ne kuraye'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.