Ban yarda a raba Nigeria ba — Rochas Okorocha

Gwamnan jihar Imo Cif Rochas Okorocha ya ce babu mutum daya daga cikin gwamnonin ko sarakunan kabilar Igbo ta kudu maso gabashin Nigeria dake goyon bayan fafutukar kafa kasar Biafra.

Kiraye-kirayen aware da kuma zargin rashin adalci a karkashin mulkin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu ‘yan kabilar ta Igbo ke yi na karuwa a kasar.

Ko a kwanakin baya ma, sai da shugaban kungiyar MOSSOB,mai fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya yi wani gangami inda ya jaddada kiran warewa daga Najeriya.

A wata hira da BBC, Cif Okorocha gwamnan jihar Imo a yankin kudu maso gabashin Najeriya inda kungiyar take ya ce da farkon fari ma batun cewa gwamnatin Muhammadu Buhari na nuna banbanci bai taso ba.

Gwamna Okorocha ya ce babu zancen cewa ba a damawa da ‘yan kabilar Igbo a gwamnatin kasar, kodayake ya akwai bukatar a kara jan ‘yan kabilar tasa a jiki.

” Ai muna da ministoci, muna da wasu da ke kan wasu manyan mukamai, akwai abubuwan da ya kamar gaskiya a duba, bai kamata ace ba a yi da Ibo ba.”

Cif Okorocha ya ce in dai batun mukamai ne a wasu lokutan akwai abubuwan da ake dubawa ba wai kawai batun kabilanci ba. Ya kuma kara da cewa ;

” Misali kamar yadda aka bayar da mukaman manyan hafsoshin sojin kasar, an yi la’akari da matsalar Boko Haram kan me za a yi don samun wanda zai shawo kan matsalar.”

Kan batun da ake yi cewa gwamnonin yankin kudu maso gabashin Nijeriyar na mara wa Nnamdi Kanu baya a fafutikar da yake yi ta kafa kasar Biafra, gwamna Rochas Okorocha ya musanta da cewa sam hakan ba gaskiya bane.

”Tambayata a nan ita ce, kana ganin a zama na na Rochas haka, sai Nndamdi Kanu zai zo ya kira ni yaki kuma in bi shi?, ka san ba mai yiwuwa bane”, babu wani gwamna ko basarake a kudu maso gabashin Nijeriya da ke goyon bayan Ndamdi Kanu da fafutikar da yake yi ta raba Nijeriya.” in ji Rochas.

Asalin Labari:

BBC Hausa

947total visits,6visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.