Bankuna a Zimbabwe za su fara karbi dabbobi a jingina

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya saka hannu kan wata sabuwar doka da za ta ba kananan masana'antu da 'yan kasuwa damar su bayar da dabbobi da wasu kayan amfani a gida a zaman jingina wajen samun bashi.

Hukumomin kasar dai sun ce an kafa dokar ne domin shawo matsalar rashin jari da kananan masana’antu ke fuskanta sakamakon halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Wannan dokar ta bai wa bankuna kasuwanci a Zimbabwe damar su karbi dabbobi kamar shanu, da awaki, da kuma tumaki a zaman jingina wajen bayar da rancen kudi.

Haka ma za ta ba su damar karbar wasu kadarorin kamar ababen hawa, da akwatunan tallabijin da na’urorin sanyaya abubuwa da kwamfutoci da sauran abubuwan amfani a gida a zaman jingina.

An yi wannan dokar ne saboda lura da yadda Kananan masan’antu a kasar ke fadi-tashi wajen samun abubuwan da za su iya amfani da su a zaman kadara wadda za su iya jinginarwa domin samun bashi daga bankuna.

Galibin masana’antu da manyan shagunan kasar a yanzu ba su da rijista da gwamnati kuma ba su da kadarorin da suke iya jinginarwa domin samun bashin.

Don haka yanzu mahukuntan kasar suka ce yanzu ana iya karbar kadarorin da ake iya dauka daga wannnan wuri zuwa wancan a zaman jingina muddin an kimanta kadarinsu kuma an yi musu rijista a kundin babban bankin kasar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

908total visits,1visits today


Karanta:  Me ya sa shugabannin Afirka ke zuwa kasahen ketare jinya?

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.