Barayin batirin mota sun farwa Majalisar tarayya da sata

Barayin batirin mota sun farwa Majalisar tarayya ba kakkautawa, duk da cewar akawai daruruwan ma’aikatan tsaro birizik wanda ke cikin kayan aiki da ma na fararen kaya.

Rahotanni sun bayyana cewar ana samun koken satar batirin motoci, rediyoyi da karfen daga mota a duk sati da ba ya gaza biyar, a wajajen da ake ajiye mota.

Daya daga cikin irin mutanen da wannan ibtila’i ya fadawa a baya-bayannan ma’aikacin Majalisa ne, wanda aka sace masa batiri da rediyon motarsa, duk da cewar ya ajiye motar kusa da ofishin ‘yan sanda na Majalisar. Motar ta sa kirar Honda an yi kaca-kaca da ita a filin ajiye motoci wanda ke kusa da babban ofishin ‘yan sanda na Majalisa.

“Dag ajiye mota ta sai na dawo na tarar da an wargaza ta. Idan dai har hakan za ta faru a nan, to lallai ba wani waje da yake da tsaro a cikin kasar nan” – mutumin ya bayyana hakan ga mansma labarai.

 

 

Asalin Labari:

Daily Trust, Muryar Arewa

1922total visits,1visits today


Karanta:  'Yan Bindiga Sun Sace Mutum 11 a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.