Barcelona Na Neman Dan Wasan Gaba Na Manchester United Marcus Rashford Don Maye Gurbin Luis Suarez

Rashford mai shekaru 19 ya fara hasakakawa tun lokacin da aka fara ganinsa a shekarar 2016.

Duk da cewa yaron dan wasa ne, mai bugawa England tamaula tuni ya sami gurbi a cikin jerin ‘yan wasan farko na Manchester United din

Tuni shirye-shirye sukayi nisa a kulub din na Barca domin tunkarar wasani bayan da kulub din ya sayi Ousmane Dembele daga Borussia Dortmund ranar Jumma’a.

Wata kafar yada labarai dake kasar Spain mai suna Don Balon ce tayi hasashen cewa dan wasan ne buri kulub din na Barca nan gaba.

Samun dan wasan na Manchester ya sakawa Barca hannu ba abu ne mai sauki ba, don kuwa zai iya kaiwa zunzurutun kudi £185m.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

2035total visits,1visits today


Karanta:  Dan wasa daya zan saya saboda tsadar da suke yi — Mourinho

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.