Barcelona: ‘Yansanda Sun Harbe Mutum Biyar Da Ake Zargi

'Yansanda a kasar Spaniya sun yi wani gagarumin farmaki kan 'yan ta'adda, bayan wasu harbe-harbe a wurin shakatawa na garin Cambrils dake kudancin birnin Barcelona.

Mahukunta sun ce , an harbe har lahira mutane biyar da ake zargi da ayyukan ta’addanci, daure da wata damarar kunar bakin wake.

An danganta faruwar lamarin da mumman harin baya-bayan nan da aka kai a birnin Barcelona, lokacin da maharan tuka babbar wata motar daukar kaya ta cikin taron jama’a a sanannen titin Las Ramblas na birnin.

Mutum 13 ne suka mutu yayin da wasu 32 suka jikkata bayan wata babbar mota ta afka wa masu yawon bude ido a wurin shakatawa na Ramblas da ke garin Barcelona.

‘Yan sanda kasar Spaniya sun ce mutane da dama sun jikkata, yayin da aka gargadi mutane su nisanci dandalin shakatawar a kusa da Placa Catalunya.

Rahotanin da ganau suka yada sun tabbatar da mutane na gudun ceton rai, inda suke neman mafaka a kantinan da ke kusa da wurin da wuraren shan Gahawa.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito hukumomin agaji sun bukaci a rufe tashar mota da ke kusa da wurin da ta jirgin kasa.

Fira ministan kasar Spaniya , Mariano Rajoy, ya ce ‘yan ta’addar masu jihadin ne ke da alhakin kai hari a birnin na Barcelona, inda mutane fiye da dari suka samu raunuka.

Ya ce ” Ina son kalamai na na farko a daren nan a Barcelona su kasance na nuna jimami da nuna goyon baya ga wadanda harin ya shafa, ina kuma son in yi nuni da goyon bayan daukacin yan kasar Spaniya”

Asalin Labari:

BBC Hausa

463total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.