Beyonce da Jay-Z zasu sayi gidan Dala Miliyan 90

Shahararriyar mawakiyar nan ta kasar Amurka mai suna Beyonce da maigidan ta wato Jay-Z na shirye shiryen sayan wani katafaren gida da akayi wa kudi dalar Amurka miliyan casa’in ($90 million).

Idan cinikin ya tabbata Beyonce da Jay-Z zasu tare a wannan gida tare da babbar ‘yar su Blue Ivy da kuma ‘yan twagayen su wato Rumi da Sir inda zasu bar gidan su na yanzu da suke haya akan kudi dalar Amurka dubu arba’in ($40,000) a kowanne wata.

Shi dai wannan sabon gida ya samu fitarwa ne daga mai zanen nan wato Paul McClean wanda yake dauke da dakuna takwas, bandaki sha daya, sai kuma wajen shakatawa na wankan zamani (swimming pool) guda uku da ma garejin ajiyar mota guda 11 duka dai akan fili mai girman taku dubu goma (10,000 square feet).

Gidan wanda yake a garin Los Angeles na kasar Amurka zai kasance gida mafi tsada tun bayar sayar da wani da aka tabayi a kan kudi dala miliyan tamanin da hudu.

Shi dai wannan gida ya banbanta da sauran ta bangori kamar su dakunan kallo na musamman dama wajen hada wakoki. Bugu da kari babban dakin gidan yana dauke da gilashi wanda bindiga bata ratsa shi. Sannan yana da filin wasa mai girman eka 2.

1311total visits,1visits today


Karanta:  Zargin luwadi ya hana a ba ni aure — Zango

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.