Biranen da Zasu Kare Yarjejeniyar Muhalli a Duniya

Kasar Denmark ta kadadmar da wani kawancen biranen duniya da za su taimaka wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar kare muhallin da aka kulla a Paris ba tare da samun matsala ba.

Shirin wanda aka kaddamar kwanaki biyu da suka wuce bayan Amurka ta tabbatar da ficewarta daga yarjejeniyar ta Paris, zai mayar da hankali ne wajen yada bayanai da fasaha tsakanin gwamnatoci da ‘yan kasuwa da kuma shugabannin al’umma.

Ofishin Firaministan Denmark Lars Lokke Rasmussen ya ce, wadanda suka amince su shiga cikin wannan tafiyar da aka kaddamar a birnin New York sun hada da kungiyar Global Goals 2030 da kasashen China da Indonesia.

Sanarwar ta ce, shirin ya samu goyan bayan manyan birane 90 na duniya wadanda suka mallaki kashi daya bisa 4 na tattalin arzikin duniya baki daya, kuma daga cikin su akwai manyan biranen Amurka 12.

Sanarwar ta ce, wannan kawance zai kafa cibiyarsa a birnin Washington DC a watan Janairu mai zuwa, kafin gudanar da taronsa na farko a watan Nuwamba.

Asalin Labari:

RFI Hausa

975total visits,5visits today


Karanta:  Kim Jong-un Ya Ce Trump Na Da Tabin Hankali

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.