Boko Haram: ‘An kashe masunta 31 a Baga’

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe wasu masunta 31 a garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno a arewacin Najeriya.

 

 

 

 

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce wannan hari na nuna cewa har yanzu mayakan kungiyar na kai hare-hare masu muni da kashe mutane a yankin tafkin tekun Chadi.

Sai dai gwamna Shettima ya ce har yanzu jami’an tsaro ba su tabatar da rahoton harin ba.

Ya ce shi ma ya samu kiran waya ne daga wasu da ke yankin, wadanda suka shaida lamarin, suka kuma tabbatar masa da hakan.

Amma ya nuna matukar damuwarsa kan abin da ya kira ci-gaba da ayyukan ‘rashin tausayi’ da mayakan ke yi a arewa maso gabashin kasar.

Gwamna Shettima ya yaba wa rundunar sojin kasar kan kokarin da take na dawo da zama lafiya a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Najkeriya, NAN, ya ruwaito cewa, ko a ranar 5 da 6 ga watan Agustan nan ma, mayakan Boko Haram sun kai wasu hare-hare guda biyu kan masunta a wasu garuruwa na Baga.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1134total visits,1visits today


Karanta:  Adamawa: Tashin Hankali Tsakanin Fulani Makiyaya Da ‘Yan Yankin Kwateh

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.