Boko Haram ta kashe mutane kasuwar Konduga

Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa, kungiyar Boko Harm ta kaddamar da hare-haren kunar bakin wake a karamar hukumar Konduga, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 27.

Maharan su tayar da bama-bamai guda biyu a wata kasuwa da ke karamar hukumar kuma a dai dai lokacin da jama’a ke tsaka da cin kasuwancinsu a yammain wannan Litinin kamar yadda wakilinmu, Bilyaminu Yusuf ya tabbatar mana.

Bam na uku ya tashi ne a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin na Kondugan kamar yadda Yusuf ya shaida mana.

 

Ana fargabar cewa, adadin wadanda suka mutu ka iya karuwa saboda munin farmakin.

Garin Konduga mai tazarar kilomita 30 daga birnin Maiduguri na daya daga cikin yankunan jihar Borno da suka fi fama da hare-haren Boko Haram, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

Asalin Labari:

RFI Hausa

746total visits,1visits today


Karanta:  An samu fashe-fashen bama-bamai a Maiduguri

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.