Boko Haram ta lalata gidaje miliyan 1 a Borno

Gwamnatin jihar Barno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta bayyana cewa, kungiyar Boko Haram ta lalata gidajen da suka kai miliyan guda da kuma azuzuwan makarantu 5,000 a fadin jihar.

 

 

 

 

Babban sakataren sake gina-gidajen da aka rusa, Yarima Saleh ya bayar da adadin ga manema labarai, in da ya ke cewa an yi asarar dukiyar da ta kai kusan tiriliyan biyu a rikicin na shekaru 6.

Alkaluman da jami’in ya bayar sun nuna cewa, kungiyar ta kona gidaje 986,453 da makarantu 5,335 da asibitoci 201 da gidajen samar da ruwan sha 1,630 da injinan samar da wutar lantarki 726.

Jami’in ya ce, ofisoshin jama’a da ofishin ‘yan sanda da gidan yari 800 kungiyar ta lalata, abin da ya mayar da kananan hukumomi 22 daga cikin 27 wadanda ba za a iya aiki a cikin su ba.

Asalin Labari:

RFI Hausa

630total visits,4visits today


Karanta:  A Kano 'Yan Najeriya Sun Yi Tsokaci Kan Dawowar Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.