‘Boko Haram ta sa mata fiye da 80 yin kunar bakin wake’

Kungiyar Boko Haram ta yi amfani da mata 'yan kunar bakin wake fiye da wadanda ko wacce kungiyar ta-da-kayar-baya ta taba yi tarihi, kamar yadda wani rahoto da kwalejin sojin Amurka ta fitar ya ce.

Kungiyar ‘yan tawayen Tamil Tigers ta kasar Sri Lanka ta yi amfani da mata ‘yan kunar bakin wake 44 a tsawon shekara 10, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Wani bincike daga kwalejin West Point ya ce an kai hare-hare fiye da 400 tun daga shekarar 2011, kuma yawancinsu a yankunan arewa maso gabashin Najeriya, da jamhuriyar Nijar da Chadi da kuma Kamaru.

Har ila yau, rahoton ya ce fiye da rabin hare-haren, ana amfani da mata ko ‘yan mata ne wajen kai su.

A bana kadai, “mayakan Boko Haram sun yi amfani da mata yawancinsu ‘yan mata fiye da 80 wajen kai harin kunar bakin wake.”

Rahoton ya ce amfani da mata wajen kai hare-haren ya karu ne tun bayan da masu tayar da kayar bayan suka sace ‘yan matan sakandiren Chibok a shekarar 2014.

An amfani da mata wajen kai hare-haren ne saboda ba a fiye zargin mata da aikata wani abu makamancin haka ba, an fi zargin maza wajen haka.

‘Yan kunar bakin waken dai na kai hare-hare ne a wurare kamar kasuwanni da masallatai da kuma sansanin ‘yan gudun hijrar da aka gina na wucin gadi.

Hakazalika, rahoton ya kiyasta cewa an kashe kusan mutum dubu biyu a hare-haren kunar bakin wake.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1044total visits,2visits today


Karanta:  Fulani 54 aka kashe, 15 kuma sun bata a Kaduna - Miyetti Allah

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.