Borussia Dortmund ta rasa inda Dembele yake

Kociyan Borussia Dortmund ya ce dan wasansu da Barcelona ke nema fafurfafur Ousmane Dembele, domin maye gurbin Neymar bai halarci atisayen kungiyar ta Jamus ba a yau Alhamis.

Peter Bosz ya ce kungiyar ta Bundesliga ta kasa samun wani bayani ko ji daga dan wasan na gaba na Faransa mai shekara 20.

Kociyan ya ce sun yi kokarin ji daga gareshi amma abin ya gagara, suna kuma fatan ba wani mummunan abu ne ya faru da shi ba.

Dembele, wanda ya yi wa kasar Faransa wasa sau bakwai, rahotanni da cewa Barcelona son sayensa a kan fan miliyan 135 domin maye gurbin Neymar.

A makon da ya wuce ne Barcelona ta sayar da dan wasan gaban na Brazil ga Paris St-Germain a kan kudin da ba a taba sayen wani dan kwallo ba a duniya, fam miliyan 200.

Dortmun ta sayi Dembele ne daga Rennes ta Faransa a watan Mayu na 2016, kan yarjejeniyar shekara biyar

Asalin Labari:

BBC Hausa

778total visits,1visits today


Karanta:  Za a gwada lafiyar Lukaku a Man United

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.