Buhari bai saba wata doka ba saboda jinyar da yake yi a Birtaniya-Majalisa

Majalisar Dattawa jiya ta ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai karya doka ba saboda dadewar da ya yi ba ya kan aiki sakamakon jinyar da yake yi a kasar Birtaniya.

Majalisar Dattawa jiya ta ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai karya doka ba saboda dadewar da ya yi ba ya kan aiki sakamakon jinyar da yake yi a kasar Birtaniya.
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa wasu kungiyoyi sun gudanar da zanga-zangar neman shugaban kasar ya dawo kan aiki ko kuma ya yi murabus.
A wata takardar sanarwar da Mai Magana da Yawun Majalisar, Sanator Aliyu Sabiu Abdullahi ya fitar ta nuna cewa “Shugaban Kasa bai karya wata doka ba saboda haka ba mu ga dalilin cece-kucen da wasu ke yi ba. Wadanda suka shirya zanga-zangar sun yi ne don su yi amfani da zaman lafiyar da kasar ke ciki su cimma manufarsu ta neman a sansu”.
Sanarwar ta kara da cewa “Mu a majalisa mun gamsu babu wata baraka ko wani gibi. Gwamnatin Tarayya tana aiki. Mukaddashin Shugaba Kasa, Yemi Osinbajo yana tafiyar da shugabancin da ya dace. Saboda haka ba mu ga dalilin yin wata zanga-zanga ba”.
Sanarwar ta ci gaba da cewa “Duk ’yan Najariya a yanzu kamata ya yi su ci gaba da yin addu’a don ganin shugaban ya dawo lafiya. Mu a majalisa mun yi murna da labarin da gwamnonin da shugabannin jam’iyya suka bayar wadanda suka ziyarce shi kwanannan a Birtaniya. Mun san cewa zai dawo kwanannan ya ci gaba da gudanar da jagorancin jama’armu da sauran kasashen Afirka”.
“Saboda haka muna kira ga masu zanga-zanga su daina, su bi sawun sauran ’yan Najeriya na yi wa shugaban kasa addu’a da mukaddashin shugaban kasa da kasa baki daya a cikin halin da take ciki”. Inji sanarwar.
Asalin Labari:

Aminiya

766total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.