Buhari Ya Bukaci Kawo Karshen Kisan Kare Dangi a Myanmar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci shugabannin kasashen duniya da su yi Allah-wadai da kisan kare dangin da sojojin Myanmar ke yi wa ‘yan kabilar Rohingya, akasarinsu Musulmi.

Buhari ya bukaci haka ne a yayin gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya na 72 da aka fara gudanarwa a birnin New York na Amurka.

Buhari ya alakanta rikicin jihar Rakhine ta Myanmar da kisan kare dangin da aka gani a Bosnia a shekarar 1995 da kuma Rwanda a shekarar 1994.

Shugaba Buhari ya ce, babu yadda kasashen duniya za su ci gaba da zura idanu kan wannan tashin hankali da ya tilasta wa mutanen Rohingya dubu 420 neman mafaka a Bangladesh.

Tuni dai Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Dunliya Antonio Guterres, ya bukaci mahukuntan Myanmar da su dauki matakin magance rikicin kasar.

A ranar Alhamis mai zuwa ne, mataimakin shugaban Myanmar, Henry van Thio zai hau minbari don gabatar da jawabi a zauren na Majalisar Dinkin Duniya, bayan jagorarar gwamnatin kasar, Aung Sang Suu Kyi ta ki halartar taron na bana.

Asalin Labari:

RFI Hausa

528total visits,3visits today


Karanta:  Hadaddiyar kungiyar matasan arewaci Nigeria ta janye umarnin korar yan kabilar Igbo bisa wasu sharudda

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.