Buhari ya cika kwanaki 100 na jinya a London

Yau kwanaki 100 cur da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma birnin London don ci gaba da duba lafiyarsa, yayin da al’ummar kasar ke ci gaba da cece-kuce kan tafiyarsa.

Tun bayan tafiyarsa a ranar 7 ga watan Mayun wannan shekarar, fadar shugaban kasar ke ci gaba da fitar da sanarwa akai-kai, in da ta ke bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa, shugaban na samun sauki daga larurar da ya ke fama da ita kuma ana saran komawarsa kasar a kowanne lokaci.

An yi ta yada hotunan da shugaban ya dauka tare da wasu ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnatin kasar da suka ziyarce shi a London.

An dai yada hotunan ne da zimmar kwantar da hankulan ‘yan kasar da ke son sanin ainihin halin da shugabansu ke ciki.

Wasu daga cikin wadanda suka ziyarce shi da suka hada da mukaddashin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo sun nanata cewa, Buhari na samun sauki kuma zai koma Najeriya nan bada jimawa ba.

Masu taimakawa Buhari a fadar gwamnatinsa sun ce, shugaban zai koma gida da zaran likitocinsa sun ba shi umarni kan haka.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da ainihin larurar da shugaba Buhari ke fama da ita, yayin da wasu ‘yan kasar ke gudanar da zanga-zangar ko dai shugaban ya dawo ko kuma ya yi murabus.

Asalin Labari:

RFI Hausa

600total visits,1visits today


Karanta:  Sojojin Ruwan Najeriya Sun Isa Yankin Niger-Delta

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.