Buhari ya gana da ma’aikatan sa a London

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da wasu daga cikin jami’an gwamnatin sa ranar Asabar a birnin London dake kasar Birtaniya inda ya shafe fiye da wata uku yana jinya, ya gana da Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, mataimakan sa kan harkokin yada labarai Femi Adesina da Mallam Garba Shehu.

A cikin tawagar har ila yau, akwai mataimakiyar sa ta musamman kan harkokin ma zauna kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa da kuma maitaimakama sa kan kafofin sadarwa ta zamani Lauretta Onochie.

Da yake jawabi a yayin ganawar, Shugaba Muhammadu Buhari yace “Na kula ya kamata na bi umarnin likita na maimakon ace nine nake bayar da umarni. Anan, likita ke da ragama”.

3651total visits,3visits today


Karanta:  Shugaba Buhari zai samar wa matasa 360,000 aikin yi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.