Buhari Ya Halarci Sallar Jumma’a A Yau Ya Kuma Gana Da Gwamnoni A Gidansa Na Aso Rok

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci sallar Jumma’a tareda ‘yan uwa Musulmi a yau din nan a babban masallacin Juma’a dake gidan gwamnati.

Cikin wadanda suka halarci sallar jumma’ar tare da Shugaba Muhammadu Buhari sun hada da gwamnonin jihohi da manyan jami’an gwamnatin tarayya.

Sai dai an hana masu daukar hoto daukar hoton sallar jumma’ar da shugaba Buharin da jami’an gwamnatin sa suka halarta.

Tun da fari dai da safiyar nan shugaban ya gana da  shugabannin jami’iyarsa ta APC da shugabannin jam’iyar adawa ta PDP

Daga bisani kuma ya gana da gwamnonin jihohin kasar  a fadarsa ta Aso Rok din dake gidansa na Abuja.

Ya dai shaidawa gwamnonin cewa soyayyar da ‘yan kasa Nijeriya suka nuna masa ya kara masa karsashi.

Shugaba Buhari ya dawo daga Burtaniya ran Asabar inda yayi hutun rashin lafiya.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

500total visits,1visits today


Karanta:  Wasu Masallata 2 Da Dan Sanda Daya Sun Rasa Ransu Sakamakon Kutsawar Wata Babbar Motar Itace Cikin Taron Idi A Ijebu Igbo.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.