Buhari Ya Kaddamar da Kwamitin Duba Tsarin Albashin Ma’aikata

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin mutane 30, wadanda zasu yi nazari da yin tsari na sabon tsarin albashin ma’aikatan kasar mafi kankanta, daga Naira dubu 18 da yake a yanzu zuwa wani kima da ya wuce haka.

A lokacin da shugaba Buhari ke kaddamar da kwamitin wanda ya hada da gwamnoni da ministoci da kungiyoyin kwadago da na ma’aikata, ya ce wajibi ne a kafa wannan kwamiti a dai-dai lokacin da Najeriya ke ganin lokaci yayi ta bi jerin kasashen duniya, da za a inganta tsare-tsaren albashi na ma’aikaci saboda muhimmancin sa ga ci gaba.

Shugaban Buhari ya ce “dukkan mu mun sani cewa tsohon tsarin mafi kankancin albashi na ma’aikatan Najeriya ya tsufa, don haka ya kamata mu kafa wannan kwamiti da muka tsara a yanzu da zai sake duba albashin da ya kamata a baiwa ma’aikaci a Najeriya.”

Gwamnanan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya bayyanawa manema labaru bayan kammala kaddamar da kwamitin cewa, wannan alkawarin da shugaba Buhari yayi ne yake cikawa. Kuma su kansu gwamnoni a shirye suke, idan tsarin ya zama doka su yi biyayya wajen aiwatar da shi.

Shugaban kungiyar kwadago na Najeriya, Kwamarad Ayuba Wabba, ya bayyana cewa sun yabawa shugaba Buhari da ya yanke shawarar kafa kwamitin, kuma yana bada tabbacin cewa a shirye suke su yi sulhu na hankali tsakaninsu da gwamnati domin a fito da tsarin da zai taimakawa ma’aikata.

Asalin Labari:

VOA Hausa

2264total visits,1visits today


Karanta:  Shugaba Muhammadu Buhari Ya Ja Kunnen Jihar Filato Kan Rikice-Rikice

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.