Buhari Ya Ummarci Jami’an Tsaro Su Kawo Karshen Barazanar Hadin Kan Kasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya ummarci shugabannin jami’an tsaro kasar nan su kawo karshen duk wata barazana ga tsaron kasa tare da kare hadin kan kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ummarci shugabannin jami’an tsaro kasar nan su kawo karshen duk wata barazana ga tsaron kasa tare da kare hadin kan kasar.
Buhari ya bayanar da ummarnin ne jiya a ganawar da ya yi da membobin majalisar tsaron kasar a fadarsa da ke Abuja.
Ganawar ita ce ta farko a wata ukun da ya yi yana jinya a Birnin Landan da ke kasar Birtaniya.
Hadin kan kasar ya gamu da kalubale ne tun lokacin da Kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biyafara ta zafafa kamfe dinta na kafa kasar Biyafara.
Inda Gamaiyar Kungiyar Matasan Arewa suka bai wa ’yan kabilar Igbo wa’adin ranar daya ga watan Oktoba su bar yankin.

 

Asalin Labari:

Aminiya

476total visits,1visits today


Karanta:  Ana ci Gaba Da Samun Raayoyi Mabanbanta Game Da Sake Kame Nnamdi Kanu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.