Buhari ya yi alla-wadai da harin mujami’a a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kazamin harin da aka kai wata mujami’a da ke Ozubulu kusa da birnin Onitsha a Jihar Anambra wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12 da jikkata 18.

Fadar shugaban ta bayyana harin a matsayin kisan gillar da aka yiwa masu ibada.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Anambra, Garba Umar, ya tabbatar da adadin a harin da ake danganta shi da zargin yunkurin kisan kai tsakanin wasu ‘Yan uwa biyu mazauna Afirka ta kudu.

Mista Garba ya kuma yi watsi da jita-jitar danganta harin da Boko Haram tare da bukatar al’ummar yankin su ci gaba da gudanar da ayukansu.

Sai dai har zuwa wannan lokaci babu wani kame da aika aiwatar kan wadanda ake zargi da hannu wajen kai harin.

Asalin Labari:

RFI Hausa

733total visits,2visits today


Karanta:  An kaddamar da sashin "Nigeria for Buhari 2019"

One Response to "Buhari ya yi alla-wadai da harin mujami’a a Najeriya"

  1. ABUBAKAR SANNI   August 7, 2017 at 2:21 pm

    Allah wadai da wannan mumunan hari sannan kuma Allah yabama iyali da ‘yan,uwa hakuri kazalika munarukunka ya allah mabuwayin sarki kakawo mana agaji kakawo mana karken wainnan masifu da bala,oa nakisan gilla awannan kasa tamu me albarka Nigeria

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.