Buhari yana samun sauki – Yakubu Dogara

Kakakin Majalisar Wakilai ta Kasa Rt. Hon. Yakubu Dogara ya bayyana cewa jikin shugaba Muhammadu Buhari yana murmurewa sosai.

Kakakin Majalisar Wakilai ta Kasa Rt. Hon. Yakubu Dogara tare da Shugaban Majalisar Dattawa ta Kasa Bukola Saraki sun ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a gidan Abuja dake birnin Landan a yau Alhamis din nan.

Kamar yadda Yakubu Dogara ya bayyana a shafin sa na Twitter yace “Naji dadin yadda na ganshi. Shugaban Kasa yana cike da koshin lafiya.”

Dogara ya umarci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yiwa Buhari addu’a gami da godiya akan addu’ar su da take karbuwa da kuma samun dawowar sa gida Najeriya lafiya.

789total visits,1visits today


Karanta:  Yemi Osinbajo ya yi 'kyakkyawar' ganawa da Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.