Cameroon za ta rufe iyakarta da Nigeria

Rahotanni daga Kamaru sun ce hukumomin kasar sun gindaya dokar ta baci a yankin kudu maso yammacin kasar mai amfani da harshen Ingilishi gabannin zanga-zangar masu neman ballewa daga kasar da aka shirya yi a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba.

Wata sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta hana mutane fita daga maraice zuwa safiya, da kuma rufe kan iyakar kasar da Najeriya da sauransu.

Shugaba Paul Biya ya kuma bayar da umarnin shirya sojoji domin kare kasar tare da tabbatar da tsaro ga dukkan ‘yan kasar masu mutunta doka, in ji wata sanarwar da gwamnan yankin kudu maso yammacin kasar, Bernard Okalia Bilai, ya saka wa hannu.

Wata sanarwar ta daban da Bilai ya fitar ta bayyana ka’idojin takaita zirga-zirgar inda ya ce dokar za ta yi aiki ne daga 29 ga watan Satumba zuwa 2 ga watan Oktobar shekarar 2017, a fadin yankin kudu maso yammacin kasar.

Magoya bayan kungiyar masu fafatukar kafa kasar Kamaru ta Kudu suna son gudanar da zanga-zanga a yankin domin tunawa da samun ‘yancin Kamaru ta Kudu daga Birtaniya a ranar daya ga watan Oktoban shekarar 1961.

An dade ana takun saka tsakanin gwamnatin kasar da mutanen kudancin kasar da ke amfani da harshen Ingilishi kan abin da masu fafatuka suka kira rashin yi wa yankin adalci.

Asalin Labari:

BBC Hausa

410total visits,3visits today


Karanta:  Al'umman Igbo Sun Yi Na'am da Janye Shirin Korarsu daga Arewacin Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.