Chadi Ta Rufe Ofishin Jekadancin Qatar

Kasar Chadi ta sanar da rufe ofishin Jakadancin Qatar da ke birnin Ndjamena inda ta bukaci jami’an diflomasiyar da ke aiki ciki da su fice daga kasar cikin kwanaki 10 masu zuwa.

Kasar Chadi ta sanar da rufe ofishin Jakadancin Qatar da ke birnin Ndjamena inda ta bukaci jami’an diflomasiyar da ke aiki ciki da su fice daga kasar cikin kwanaki 10 masu zuwa.

Wannan ya biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin Saudi Arabi da Qatar, inda Chadin tare da kasashen Mauritania da Senegal ke goyan bayan Saudiya.

Jakadan Najeriya a Ndjamena Muhammad Dauda ya shaidawa RFI Hausa cewa ba su ji dadin matakin na Chadi ba, kuma a cewarsa watakila Chadi tana ganin yanke huldar ne mafi alheri a gare ta daga bukatun da ta ke samu daga Saudiya.

Tun soma rikicin diflomasiya tsakanin Qatar da Saudiya, kasashen Afrika da suka hada da Chadi da Nijar da Mauritania da Senegal da kuma Gabon suka janye jekadunsu daga Qatar.

Saudiya da wasu manyan kasashen Larabawa sun zargi Qatar da taimakawa kungiyoyin ta’adda da suka hada da al Qaeda da kungiyar IS da ke da’awar Jihadi a Syria da Iraqi, zargin da Qatar ta musanta.

Asalin Labari:

RFI Hausa

620total visits,4visits today


Karanta:  Donald Trump ya Sassauta Ra'ayinsa Kan Koriya Ta Arewa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.