Cutar da ba a Sani ba ta Kashe Mutum 62 a Nigeria

A kalla mutum 62 sun mutu a jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, bayan wata cutar da ba a san hakikaninta ba ta barke.

Wata sanarwa da ma’aikatar lafiyar jihar ta fitar ta ce wadanda suka kamu da cutar suna cin ciwon mara baya ga amai da gudawa da suke yi.

Sanarwar ta ce daga farko dai an kai wadanda suka kamu da cutar asibitin koyarwar gwamnatin tarayyar kasar da ke jihar Edo, inda aka gane cewar ba zazzabin Lassa ba ne ke damunsu.

Rahotanni sun ce cutar ta fi shafar al’ummomin Fulani da ke jihar ne, wadanda yawancinsu makiyaya ne.

Tawagar lafiya ta jihar ta je yankunan da annobar ta barke, inda suka yi bincike kan ruwan sha da hanyoyin samun abincin mutanen wajen.

Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin a duba wadanda suka kamu da cutar kyauta a asibitoci, a kuma yi gaggawar daukar matakin dakatar da yaduwarta kafin ta yi barna sosai.

Wasu rahotanni a Najeriyar na cewa hukumomi a jihar Kwara mai makwabtaka suna gudanar da bincike kan barkewar irin wannan cutar a cikin jihar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

608total visits,1visits today


Karanta:  Atiku ya kalubalanci masu cewa ya yi sata su ba da hujja

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.