Daga Africa Za’a Rika Tantance Bakin-Haure – Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, tare da wasu shugabanin kasashen turai, yayin tattaunawa da shugabannin kasashen Nijar da Chadi, Muhammadou Issoufou da kuma Idris Deby kan yadda za'a shawo kan matsalar kwarar bakin haure zuwa turai.

A lokacin zaman taron da aka gudanar a jiya Litinin a birnin Paris kan matsalar bakin haure, tsakanin wasu kasashen nahiyar Afrika da na Turai, Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bada shawarar cewa, daga sansanonnin tattara bakin hauren dake cikin kasashen Niger da Chadi za’a rika tantance ‘yan kasashen da suka cancanci zama ‘yan gudun hijira tare da basu cikakken tsaro.

Macron, yace matakin tantance bakin hauren domin sanin wandanda suka cancanci zama ‘yan gudun hijira a turai, zai fara ne daga kasashen biyu, a karkashin zura idon hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

A cewar Macron, matakin zai taimaka wajen kaucewa yadda mata da maza ke jefa kansu cikin masifa, suna ratsa yankunan dake tattare da hatsari musamman tekun Méditerraném zuwa turai”.

Zalika shugaban na Faransa ya ce, za’a hada gwiwa wajen tabbatar da tsaro, shara’a tare da samar da sojoji ga sansananonin tattara bakin hauren domin kaucewa fandarewa ko kuma ci gaba da kwararar bakin zuwa kasar Libiya, saboda gudun hakan zai kara tumbatsar sansanonin bakin hauren da tuni suka cika a can.

Asalin Labari:

RFI Hausa

648total visits,3visits today


Karanta:  Kaddamar da rundunar sojin Sahel sai da taimakon kasashen Duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.